Ina Goyan Bayan Takarar Dakta Dikko Raɗɗa Ɗari Bisa Ɗari
Saboda Cancantarsa Da Gogewarsa, Cewar Minista, Sanata Hadi Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Sanata Hadi Abubakar Sirika ya bayyana cewa yana goyan bayan dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa saboda cancantarsa.
Sanata Hadi Abubakar Sirika ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattauna wa da manema labarai a gidansa dake Katsina yau Litinin.
Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Sanata Hadi Abubakar Sirika ya kara da cewa ina goyan bayan dan takarar gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Raɗɗa ɗari bisa ɗari kuma duk da yanayin aikin da aka ba ni amana na Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya kuma na farko fuskata an ganta saboda da Dakta Dikko Raɗɗa ya je shiyyar Daura yaƙin neman zabensa a gidana ya zauna tsawon kwana biyu ya yi reras kuma na samu damar halartar taron tara masa guddumuwar kuɗi.
Sanata Hadi Abubakar Sirika ya cigaba da cewa yanzu da yake an ba ni aiki na amana, na mutum miliyan ɗari biyu da goma sha biyar kuma ban gama shi ba. Zan taho lokacin da ya kamata in taho saboda ba ni da wani dan takarar da ya wuce Dakta Dikko Raɗɗa ɗari bisa ɗari bisa ɗari.
Comments
Post a Comment