Ƙungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya ta ce ta fasa shiga yajin aikin data shelanta zata fara daga ranar Litinin sakamakon tsadar man jirgi da ake sayarwa kan N700 a kowace lita.
Shugaban ƙungiyar Airline Operators of Nigeria (AON) kuma shugaban gudanarwa na Azman Air, Faisal Abdulmunaf, shi ne ya tabbatar wa BBC Hausa a yau Lahadi cewa sun dakatar matakin nasu.
Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu.
Comments
Post a Comment