Tsohon Ministan sufurin jiragen Sama Sanata Hadi Abubakar Sirika a wata hira da yayi da yan jarida a fadar gidan sa dake garin Shargalle ya yaba wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin cigaban da gwamnatin ta samar wa kasar mu a ko wane fanni. Sanata Hadi Abubakar Sirika ya yabama al'ummar jahar Katsina da kasa baki daya bisa yadda bisa yadda suka fito bikin yata Shugaba Muhammadu Buhari murnar kammala aiki. Sirika ya kara da cewa taron da al'umma suka yi ya tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa yayi nasara a mulkin da yayi na tsawon shekara takwas. Yaci gaba da zayyano ire-iren cigaban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo ma al'umma, irin inganta tsaro, inganta noma, inganta kasuwanci, tallafawa matasa da masu karamin karfi (Npower, Trader Moni) da sauran su. Sirika yaci gaba da zayyano ire-iren cigaban da aka samu a ma'aikatar da ya jagoranta, wanda a tarihi ba'a taba samun gwamnatin da ta kawo cigaban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo ba,...